Kotu ta wanke tsohon firaministan Nijar Hama Amadou
October 6, 2012
A Jamhuriyar Nijar kotun ƙolin ƙasar ta wanke Hama Amadou shugaban majalisar dokokin ƙasar ta Nijar a yanzu kana tsohon firaministan ƙasar daga zargin yin sama da faɗi da kuɗaden tallafin ga kafofin yada labarai masu zaman kansu na ƙasar a shekara ta 2001.
Kotun ta wanke Hama Amadou bayan wani dogon zama na kimanin awoyi 14 da ta yi a yimmacin ranar Juma'a a birnin Yamai, wannan kuwa duk da ƙoƙarin da babbar mai gabatar da kara ta gwamnatin ƙasar ta yi na ganin alkalan kotun sun tuhume shi a lokacin wannan zaman na kotu. A kan wannan zargi ne dai mallam Hama Amadou shugaban jam'iyyar Lumana Afirka daya daga cikin manyan jam'iyyun da ke mulki a yau, ya tsinci kansa a gidan kurkuku na garin Kutukale a shekara ta 2008 lokacin mulkin hamaɓararen shugaban ƙasar Tanja Mamadou, inda ya kwashe watanni 10.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Mohammad Nasiru Awal