1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta umarci Hissene Habre biyan diya

Abdul-raheem HassanJuly 29, 2016

Kotun kungiyar tarayyar Afirka, ta umarci tsohon shugaban kasar Chardi Hissene Habre ya biya dala $33,000 ga duk wadanda ya cutar a zamaninsa.

https://p.dw.com/p/1JYSq
Hissene Habre Tschad Diktator
Hoto: picture-alliance/AFP/Stringer

Wata kotu ta musamman da kungiyar tarayyar Afirka ta kafa, ta umarci tsohon shugaban kasar Chardi Hissene Habre biyan diyar kudi sama da naira miliyan daya da rabi ga iyalan wadanda shugaban ya azabtar a lokacin da ya mulki kasar a shekara ta 1982 zuwa shakara ta 1990.Tshohon shugaban na Chadi na fuskantar matsin lamba daga masu shigar da kara, tun bayan da kotu ta tabbatar da laifukan cin zarafin bil'adama da ya kai ga aikata kisan gilla ga dubban fararen hula hada da aikata fyade.

A watan Mayun da ya gabata aka yanke wa tshohon shugaban da ake kwatanta mulkinsa na da kama karya, hukuncin daurin rai da rai a gidan yari. A bara ne kotun manyan laifuka ta duniya ICC ta umurci Senegal da ta gurfanar da Hissane Habre domin yi masa shari'a.