Kotu ta yi watsi da neman soke zaben Zambiya
September 5, 2016Talla
Kotun tsarin mulkin kasar Zambiya ta yi watsi da bukatar soke sakamakon zaben shugaban kasa na watan jiya na Agusta da Shugaba Edgar Lungu dan shekaru 59 da haihuwa ya samu nasara, abin da ya bayar da damar rantsar da shugaban a makon gobe na wa'adin mulki na shekaru biyar. Jagoran 'yan adawa Hakainde Hichilema dan shekaru 54 da haihuwa, ya kalubalanci sakamakon zaben da ya bai wa Shugaba Lungu nasara. Ranar 11 ga watan Agustan da ya gabta ne dai aka gudanar da zaben kasar ta Zambiya.