Kotu ta jinkirta zaben Saliyo
March 24, 2018Wata babbar kotun kasar Saliyo ta bayar da umurnin jinkirta gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka tsara a wannan Tala mai zuwa, har zuwa lokacin da za a gudanar da bincike kan zargi magudi da wani jigon jam'iyya mai mulki yake zargi abin da ya janyo ya garzaya zuwa kotun. Haka zai iya janyo kara zaman zullumi a kasar da aka samu rabuwa bisa dalilan siyasa.
An tsara gudanar da zagaye na biyu na zaben tsakanin dan takara na jam'iyyar adawa Julius Maada Bio wanda ya zo na farko a zaben da ya gabata, da kuma dan takara na jam'iyya mai mulki Samura Kamara tsohon ministan harkokin kasashen ketere. Ita dai kasar Saliyo da ke yankin yammacin Afirka ta yi fama da yakin basasa na fiye da shekaru 10, kuma duk wanda ya lashe zaben duk lokacin da aka tsara bayan takkadamar a kotu, zai maye gurbin Shugaba Ernest Bai Koroma da ke kammala wa'adin mulki na shekaru 10.