Kotu na sauraron 'yan adawar kasar Gabon
January 5, 2015Talla
A ranar 20 ga watan Disamba ne dai 'yan adawar kasar ta Gabon suka gudanar da wata zanga-zanga mai munin gaske, inda aka yi artabu tsakanin su da jami'an tsaron kasar bayan da suka bukaci yin wata zanga-zangar da ba'a bayar da izininta ba, wadda a cikin ta suke neman ficewar shugaban kasar Ali Bongo Ondimba da ya fuce daga karagar mulkin kasar, zanga-zangar da tayi sanadiyar rasuwar mutun guda a cewar Jami'an tsaron yayin da 'yan adawar suka nce mutun shidda ne suka rasu. amma dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da adadin da kowane bengare ke ikirari.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe