1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Faransa ta wanke tsohon shugaban hukumar IMF

Suleiman BabayoJune 12, 2015

An wanke Dominique Strauss-Kahn daga zargin da aka yi masa na halartar bukukuwa da mata samu zaman kansu

https://p.dw.com/p/1FgHq
Frankreich Dominique Strauss-Kahn Urteil in Paris
Hoto: Reuters/G. Fuentes

Wata kotun kasar Faransa ta wanke tsohon shugaban hukumar ba da lamuni ta duniya, IMF, Dominique Strauss-Kahn bisa zargin da aka yi masa da halartar bukuwa da aka gayyaci mata masu zaman kansu.

Masanin tattalin arzikin dan shekaru 66 da haihuwa ya girgiza kai domin nuna ya amince da hukuncin, bayan da masu gabatar da suka ce babu shaidar da ake bukata wajen ci gaba da shari'ar. A shekara ta 2011 Strauss-Kahn ya rasa mukamunsa lokacin da aka yi zargin ya yi yunkurin lalata da mai aiki a wani otel da ke birnin New York na kasar Amirka. Dominique Strauss-Kahn ya jagoarnci hukumar ta IMF daga shekara ta 2007 zuwa 2011.