Koriya ta Arewa da ta Kudu za su tattauna
January 5, 2018Mahukuntan na birnin Seoul sun bayyana haka ne sa'oi bayan da Amirka ta bayyana cewa za ta tsagaita shirin atisaye da sojan kasarta tare da takwarorinsu na Koriya ta Kudun ke yi har sai angama wasannin na Olympic.
A ranar Jumma'an nan kuma Koriya ta Arewa ta tura da sako zuwa ga takwarar tata Koriya ta Kudu inda ta ce za ta amince da shirin tattaunawar na garin Panmunjom da ke kan iyakar kasashen biyu a ranar Talata don tattaunawa kan shirin na gasar Olympic da ma tattauna alakar kasashen biyu.
Ana dai kallon duk wani shiri na tattaunawa tsakanin kasashen biyu a matsayin abu mai muhimmanci a kokari na samar da zaman lafiya tsakanin kasashen, sai dai wasu masharhanta na ganin cewa Koriya ta Arewa na son amfani da damar wajen raba kan mahukunatan na Seoul da na Washington, haka nan kuma ta rage matsin lamba da kasar ke samu tsakanin kasa da kasa, da ma neman sassauci kan tarin takunkumi da aka kakaba wa kasar ta Koriya ta Arewa.