Neman sasanta Isra'ila da Falasdinu
February 23, 2023Dakarun Isra,ila sun kai samame kan birnin Nabulus na Falasdinawa da nufin farautar wasu baraden kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Arinun Usud, wato kogon zakuna, kungiyar da Isra, ilan ke daura wa alhakin kai wa 'yan share wuri zauna jerin hare-hare a watannin baya. Tun bayan sabuwar gwamnatin Benjamin Netanyahu mai tsaurin ra,ayi da aka rantsar da ita farkon shekara, wacce ta ce babu batun tattunawa da Falasdina, kuma babu batun dakatar da gina matsuganan share wuri zauna, an hallaka fiye da Falasdinawa 200 a samamen da Isra,ila ke kai wa a yankunansu. Tuni wakilin Falasdinawa a MDD, Riyadh Mansur ya nemi MDD da ta bai wa Falasdina kariya daga abun da ya kira kisan kiyashin da Isra,ila ke musu:
"Muna bukatar kwamatin sulhu na MDD da ya aiwatar da kudirin dokar bai wa Falasdinawa kariya daga kisan kare dangin da Isra,ila ke musu ta hanyar tura dakarun kasa da kasa masu shiga tsakani." A nasa bangaren,Sakataren MDD Antoney Gotteres, yayi kira ga bangarori biyun da su mayar da wukakensu cikin kube:,
'Muna gudanar da wannan taron ne adaidai lokacin da yanayin da ake ciki a yankunan Falasdinawan da Isra, ila ke mamaye da suke kara cabewa.Tun farkon wannan shekarar, lamura a yankin ke kara yin kamari. Abun takaici ne a ce tarzoma da tashin hankali sune madadin kashe wuta da shiga tattaunawa. Domin yin haka ne ka dai muka yi ammanar zai tabbatar da zaman lafiya a dukkanin yankin."