Libiya: Samar da sabuwar ranar zabe
December 23, 2021Talla
Majalisar wakilan kasar ta ayyana cewa ba za a iya gudanar da zaben da aka shirya gudanarwa domin kawo karshen rikicin kasar na tsawon shekaru ba, inda ta ce tilas a sake daukar lokaci. Wani dan majalisar wakilan da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, an nada kwamiti da zai tattauna batun sanya sabuwar ranar gudanar da zaben. Hukumar zaben kassar dai ta bayar da ashawwarar a dage zaben har zuwa ranar 24 ga watan Janairun shekara mai zuwa ta 2022, sai dai ganin yadda ake cikin takun saka tsakanin majalisar dokoki da ke gabashin kasar da kuma gwamnati a Tripoli amincewa da ranar gudanar da zaben zai yi wuya.