Kokarin magance matsalar karancin kaji a Nijar
July 20, 2016
Kauyen na Bartcawel da ke cikin karamar hukumar Hamadallaye mai tazarar kilo mita 25 daga Yamai kenan inda matashin dan shekaru 32 mai suna Mourtala Himadou ya zaba don girka wannan masana’anta ta kiyo da sarafa kaji, a nan wani shinge ne hadi da wasu tarin injina a yayin da wasu tarin matasa ke tsaye don binciken lafiyar kajin da ake shirin shigar wa a mayanka bayan dauko su daga wurin kiyo, a ya yin da a gefe daya, wasu manyan dakuna ne biyu ake kiyon kajin a cikin su. Malam Abdoulaye Mounkaila shi ne babban jami’in da ke kula da masana’antar:
"Wannan dakunan ko wane daya yana daukan kaji dubu 27 kuma tun suna kankana ake kawosu, sannan mu yi kiwon su har kwanaki 45 zuwa 50 kafin mu kai su a mayanka masana’antar dai na a matsayin irin ta ta farko a kasar ta Nijer inda akalla ma’aikata fiye da 100, kama daga masu kiyon kaji har izuwa masu aikin yanka kajin ke aiki a ko wace rana. Kamfanin na da kayayakin zamani wanda akalla yake yanka kaji 1,500 ko wace awa:
"Idan aka yanke su, sai su shiga inda ke da ruwan zafi daga nan sai wurin da ake fige su nan kuma sai su wuce wurin da ake fede su sai wurin da ake yanke kawunansu da kafafuwa sai kuwa su isa inda ake wankewa kafin su iso a nan inda muke."
Wannan masana’antar za ta taimaka wajan rage korafin cin kaji masu sanyi da ke shigowa kasar daga kasashen waje. Tuni dai masana ke ganin cewa idan har gwamnati ta taimaka, to ba shakka za a ciyo kan matsalar karamcin cimaka inji Farfesa Djibo Hamani na jami’ar birnin Yamai da na tarar da shi ya zo sayen kajin da matashin ke samarwa:
" Idan aka basu taimako kudaden da za a samu a cikin kasa za su tsaya kuma suna daukar ma’aikata kenan suna taimakon mutane da yawa."
Sai dai wata matsalar ita ce kajin da masana’antar ke sayarwa na fuskantar kalubalen farashi inda ake sayar da su akan jika biyu da tamma 750 na CFA. a ya yin da kajin da ake fitowa da su masu sanyi daga waje ake sayarwa akan jika biyu kawai, amma kuma duk da haka kajin na samun karbuwa. Sai dai duk da wadannan nasarorin da ake gani kan wannan masana'anta da matashin ya girka, wani babban kalubale da ma’aikatar ke fuskanta shi ne na karamcin wutar lantarki da kuma tsabagen kudaden haraji, abubuwan da matashin ya ce zai iya kai ka karya manufarsa ta yaki da karamcin cimaka da matsalar shigowa da kaji daga waje uwa uba samarwa matasa aikin yi.