Shahararren mawakin gargajiya a Najeriya marigayi Alh. Dr. Mamman Shata Katsina, ya ce babu mai gadon sana'arsa ta waka, ko da za a samu sai an dau lokaci. Amma dansa Alh. Sunusi Shata ya ce ya gaji mahaifinshi don tsare mutuncin gidansu da sana'ar mahaifinshi.