Kira don bude wurin kwanan daliba a Yamai
April 13, 2017Jam'iyun adawa da kungiyoyin fararen hula na Jamhuriyar Nijar sun yi kira ga gwamnati da ta bude wurin kwanan dalibai da ta rufe bayan arangama da suka yi da jami'an tsaro a ranar Litinin da ta gabata. Cikin wata sanarwa da suka fitar a birnin Yamai sun kuma bukaci a saki daliban da ke tsare da tare da bata lokaci ba. Hakazalika sun yanke shawarar shirya zanga-zangar lumana domin kare 'yancin neman ilimi a kasar.
Ita ma Hukumar kare Hakkin Bil Adama ta Nijar CNDH ta mika irin wannan bukata, inda ta ce bude wurin kwanan daliban zai samar da kyakkyawan yanayin karatu a jami'ar. Sai dai kuma ta gargadi dalibai da su guji lalata kadarorin gwamnati idan suna zanga-zanga.
Mutane biyu ne suka rasa rayukansu a zanga-zangar daliban, yayin da 108 suka sami raunuka, sannan aka kame 313 ko da shike an saki 57 daga cikinsu.