kiki-kaka a majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar
March 4, 2014'Yan Nijar sun jima suna jiran wannan zama da majalisar dokokin Nijar ta yi, kasancewa ya zo ne a daidai loakcin da guguwar sabani ke ci gaba da kadawa a tsakanin bangarorin siyasa. 'Yan kasar dai da dama na ganin cewar zai kasance mai cike da cece-kuce. Bisa ga dukkanin alamu ma dai, 'yan siyasar Nijar ba su ba wa mara da kunya ba. Hasalima dai a cikin jawabinsa na bude zaman taro kakakin majalisar dokokin Hama Amadou ya mayar da hankali a kan batun harin bindigar da aka kai a gidansa a tsakiyar watan jiya wanda ya bayyana a matsayin wani koma bayan demokaradyiya a Nijar.
"Demokaradiyarmu ta fara lalacewa don bayan shekara 25 muna siyasa muna jayeyya, amma ko rana guda babu wanda aka taba ko aka kashe. Kenan da an koma harbe harbe wata rana kashe mutun za a yi. Wasu ma sun ce wai Hama da kanshi ne ya yi shi. To haukan iko zai sa da kaina in dauki bindiga ko kuma in sanya wani ya harba bindiga a gidana in kashe dana? To Allah ya rabani da iko idan na yi wanann abu."
Harin gidan Hama Amadou ya kunno kai a majalisa
To sai dai wannan batu da shugaban majalisar dokoki ya ambato a cikin jawabin nasa na bude taro bai yi wa bangaran masu mulkin dadi ba. Saboda haka ne Honorable Zakari Oumaru shugaban rukunin 'yan majalisar dokoki na bangaran masu rinjaye ya mayar da martani.
"Mu muna jiran jawabi wanda ya shafi halin da Nijar ta ke ciki na yaki da talauci da yanayi na tsaro wanda ba shi da kyau. Maimakon haka, abun ashsha ya kawo, zancen da ya ke kotu maimakon ya bari koti ta ci-gaba da aikinta. Sai ya zo nan gaban baki wanda ya gayyata ya kawo wanann zancen wanda a gurinmu zance ne na siyasa wanda dukkan 'yan Nijar sun san a kan wace manufa aka yi shi."
'Yan majalisa na shirin tsige kakakin majalisar Nijar
Sai dai wasu rahotanni na cewa bangaren masu rinjaye na da niyyar neman tsige shugaban majalisar dokokin Nijar daga kujerarsa. Tuni ma suka samu adaddin Kuri'u 76 da za su basu damar cimma wannan buri. A kan haka ne na tambayi Honorable Zakari Omaru ko mene ne gaskiyar wanann labarin?
"Mu dai mun sa ido muna kallon yanda shugaban majalisa zai tafiyar daayyuka wadanda doka ta aza masa. to amma halayen da mu ke gani yanzu ba halaye ba ne na neman zaman lafiya. Ta kan yiwu ya kaimu inda ba mu so kai ba, amma dai yanzu ta rage gareshi."
Sai dai da ya ke mayar da martani shugaban majalisar dokokin Hama Amadou cewa ya yi ya na da wannan labari. Amma a shirye ya ke ya karbi duk wani hukuncin da Allah ya kadarra.
"Mukami Allah ya ke badawa, Allah ya ke amshewa. Kenan ni wajena komi na wajen Alah,. kuma an haifeni shugaban majalisar dokoki ne ? Kafin ni mutun nawa ne su ka zauna cikin wannan kujerar? kenan kuma abin da ban gada ba wajen babana zan ce wani abu ne? Ai kun ga lokacin da aka fiddani daga mukamin framinista lokacin "motion de censur" kun ga na yi wani abu na hasala ne ?"
Daftarin dokoki 39 ne gwamnatin ta gabatar wa majalisar dokokin Nijar, daga ciki har da ta batun bai wa 'yan Nijar mazauna kasashen waje damar shiga zabe a zabuka masu zuwa.
Mawallafi: Gazali Abdou Tassawa
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe