Katsina:Matashin mai diploma ya kama sana'a
June 12, 2019Talla
Kasuwar Ajiwace da ke Jihar ta Katsina na daya daga cikin kasuwannin da matashin Ibrahim Isyaku ke baje kolin takalmansa dan sayarwa, matashin ya shaida wa DW gundarin abin da ya nutsar da shi kama sana'ar takalman bayan kammala karatunsa tsawon lokacin babu aikin yi. Matashin ya ce a dalilin da ya sa ya shiga sana'ar saboda rashin aikin yi bayan ya kammala karatunsa.