1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya na shirin nada sabon firaiminista

Ramatu Garba Baba
February 10, 2022

Bangaren Khalifa Haftar ya amince da zabin majalisar dokokin Libiya na dora Fathi Bashagha a matsayin sabon firaiministan da zai maye gurbin Abdulhamid al-Dbeibah.

https://p.dw.com/p/46p2G
Libyen | Fathi Bashagha kandidiert als Präsident
Majalisar Dokokin Libiya ta zabi Fathi Bashagha Hoto: Hazem Turkia/AA/picture alliance

Bangaren Khalifa Haftar na Libiya ya amince da matakin Majalisar Dokokin kasar na zaben Fathi Bashagha a matsayin wanda ake kyautata zato zai zama sabon firaiministan kasar. Sanarwar daga hannun Kanal din ta fito ne jim kadan da majalisar ta cimma wannan matsaya bayan da daya dan takarar mukamin firaiministan ya janye takararsa. Bashagha tsohon Ministan harkokin cikin gidan kasar. 

Babu dai karin bayani ko majalisar za ta kada kuri'ar kafin tabbatar da shi a hukumance. Firaiminista na wucin gadin kasar Abdulhamid al-Dbeibah, ya kekashe kasa inda ya ce, ba zai amince da shirin tsige shi da majalisar tayi ba.

An shiga wannan takun sakan da al-Dbeibah dan shekaru sittin da uku da haihuwa, bayan da ya ki cika alkwarin da ya dauka na kauracewa shiga takarar shugabancin kasar, matakin da ya ba shi damar darewa kujerar firaiministan da yake a yanzu, ana ganin yayi amai ya lashe bayan da ya kudiri anniyar shiga takara daga baya, lamarin da ya haifar da rudanin siyasa a kasar da ake kokarin kawo karshen rikicin da ya dabaibayeta na sama da shekaru goma.