1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira na neman mafaka

May 22, 2020

'Yan gudun hijira sama da 1,500 da hare-haren 'yan bindiga ya tarwatsa a jihar Katsina mafi akasari mata da kana nan yara, na neman mafaka.

https://p.dw.com/p/3cejr
Symbolbild Nigeria Bama Flüchtlinge
Salla a sansanin 'yan gudun hijiraHoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

Da yawa daga 'yan gudun hijirar dai na kwanciya a wani filin wasu kuma sun nemi mafaka a gidajen jama'a. Hakan dai na zuwa ne lokacin da gwamnatin Najeriya ta tura jami'an tsaro domin yaki da 'yan bindigar. Irin yadda 'yan bindigar ke kaddamar da hare-hare musamman ga mazauna yankunan karkara ne dai, ke tilastawa al'umma watsewa. Su kan lalata gidaje su kona dukiya su kore dabbobi idan sun kai harin. Yanzu dai wadannan 'yan gudun hijira babu abin da suke bukata illa daukin gaggawa.

Wadannan 'yan gudun hijira dai wasu na zaune a cikin birnin Katsina wasu kuma na kanan nan hukumomin da hare-haren bai shafa ba, koda yake kungiyoyi na ci gaba da kai wa musu dauki.
Hajiya Murja Saulawa mamba ce a wani dandalin sada zumunta na WhatsApp, ta ce irin halin da suka ga 'yan gudun hijirar na ciki ya sanya sun yi shawarar hada kudie domin tallafa masu. Baya ga kungiyoyin da ke tallafawa 'yan gudun hijirar a jihar Katsina, akwai daidaikun mutane kuma da ke tallafa musu musamman ma da wurin kwana da abinci.

Sai dai a nata bangaren gwamnatin jihar Katsinan ta ce tuni ta bayar da umarnin a duba halin da 'yan gudun hijirar ke ciki domin a tallafa musu da ma duba yiwuwar komawa garuruwansu, ganin sun dau matakan samar da zaman lafia a cewar Mustafa Muhd Inuwa shugaban kwamitin tsaro kuma sakataren gwamnatin jihar. Yanzu dai za su yi bukukuwan sallah a sansanin 'yan gudun hijira, abin da duk magidanci ke fatan ganin ya yi a gidansa tare da iyalinsa.

Jemen Leid der Kinder
Yara da mata na bukatar tallafiHoto: Getty Images/AFP/T. Karumba