Najeriya: Mahara sun halaka mutum 13
May 21, 2019Talla
An kai harin ne a garin 'Yar Gamji da ke karamar Hukumar Batsari a jihar ta Katsina. Wani ganau ya shedawa wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaba cewa, lamarin ya faru ne bayan saukar ruwan sama a yankin, inda manoma suka bazama dan yin aiki a gonakinsu kuma ba zato ba tsanmani maharan suka bude musu wuta.
Jahar Katsina da ke makwabtaka da jahar Zamfara ta fada cikin yanayi na rashin tsaro a baya-bayan nan bayan da matsalar sace mutane da yin garkuwa da su don neman kudin fansa ya kara yin kamari a sassan kauyukan Zamfaran.