Matashi mai sana'ar hotuna a Katsina
January 23, 2019Talla
Wannan matashi Ibrahim Rafuka ya kammala karatunsa ne tun shekara 2013 ya nemi aiki kuma bai samu ba, shi ya sa ya yanke shawarar nema wa kansa mafita kuma a cewarsa ya ga amfanin hakan: "Bayan na kammala karatuna, na Diploma kuma na yi HND kasancewar ban samu aiki ba sai na yi tunanin cewar yana da kyau na yi wata sana'a don samun aiki ba tare da na yi dogaro da wani ba. Wannan shi ya bani damar na koyi sana'ar daukar hoto na bidiyo, na samu nasarori sosai saboda na yi aure kuma ina dogaro da kai ina taimakon wasu musamman kannena wajen sha'anin karatunsu. " Sai dai matashin dukka kalubalen da yake kuskanta bai hanasa cigaba da sana'ar ba ganin duk lokacin da ya fita yakan samun abin da zai korewa bakinsa kuda dama iyalinsa.