Katsina: Mai sana'ar tabarmar leda
February 20, 2019Talla
Wani matashi a jihar Katsinan Najeriya da ya kammala karatunsa na jami'a ya rungumi sana'ar yin tabarmar leda. Matashin ya ce duk da nakasar da ya ke da ita bai tsaya yin bara ko neman gwamnati ta bashi aikin yi ba, ya tashi tsaye wajen neman na kansa kuma a halin da ake ciki wannan sana'a ta rufa masa asiri har ma tuni ya fara daukar wasu matasa 'yan uwansa aiki.
Matashin yace ya sami nassarar koyar da matasa maza da mata su kimanin 50 sana'ar ta yin tabarmar leda.
Sai dai yace yana fuskantar kalubale wajen rashin kayan aiki na zamani da kuma rashin tallafi daga gwamnati.