Katsina: Bunkasa harkar noman rani
February 27, 2019Talla
Wannan matashi dai ya ce bayan ya kammala karatu ya ga cewar babu abin da ya kamata ya yi shi ne ya kama dogaro da kansa, matashin mai sunan Abdullahi Bature ya ce, ya yanke shawarar kama sana'ar noman rani dan amfani kansa da sauran al'umma: "Babban abin da ya sa na kama noman rani shi ne bayan na kammala karatuna na ga ya kamata na kama wata sana'a wadda zan dogara da kaina saboda na lura dogaro ga gwamnati ba biyan bukata." Wannan matashi dai ya kwashe kusan shekaru biyar yana wannan sana'a ta noman rani a katsina.