Sana'ar kiwon kaji a Katsina
April 17, 2019Matashi Buhari Abdulhadi Katsina ya ce ya rungumi wannan sana'a ce bayan kammala karatunsa na jami'a inda ya ce yin hakan shi ne mafi alheri gare shi maimakon neman aiki na gwamnati ko kamfani wanda mafi akasari ba ya samuwa. Tuni dai a cewarsa sana'ar ta fara bude masa hanyoyi na samun abin biyan bukatun rayuwa
"Abun da ya bani sha'awar kiwon kaji shi ne bayan na gama karatuna ina zaune ana faman neman aiki bai samu ba naga gara in yi tinanin me ya kamata in fara dan in dogara da kaina bayan nayi wannan nazari na fada sana'ar kiwon kaji"
Sakamakon wanna sana'a ta kiwon kaji da mashi Buhari ya runguma ya ce ya samu nasasori matuka gaya ta yadda har ya kaiga yana farantawa wasu rai
"Cikin wannan sana'a naje na kara karatu kuma bayan haka nike daukar dawainiyar gidammu da kuma kannena da kuma dukkanin 'yan uwana da ma masu bukatar taimako kuma nayi mahalli ga abun hawa sannan yanzu har na kara bude wani kasuwancin".