Katanga tsakanin Amirka da Mexico
February 4, 2019Talla
Ma'aikatar tsaron Amirka ta sanar da sake tura dakaru 3750 zuwa kan iyakar kasar da Mexiko, abin da ya kara yawan dakarun Amirkan da ke kan iyakar kasashen biyu zuwa 4350.
Baya ga tsaron kan iyakar, sojojin kuma za su shimfida wayoyi masu kaya har na tsawon kilomita 240, a kokarin hana 'yan ci-rani shiga Amirkan ba bisa ka'ida ba.
A cewar ma'aikatar tsaron ta Amirka, sojojin za kuma su sanya kamarori na tafi da gidanka domin hangen masu son tsallakawa zuwa Amirkan.