1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An amince a sassauta dokar hana fita

Ramatu Garba Baba
August 9, 2019

An shirya sassauta dokar hana fita a yankin Kashmir don bai wa al'ummar Musulmi da ke da rinjaye a yankin damar gudanar da sallar Juma'a duk da yanayi na zaman dar-dar da ake ciki.

https://p.dw.com/p/3NceF
Indien | Ramadan in Kaschmir
Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS

Rahotannin daga kasar Indiya sun nuna cewar za a sassauta dokar hana fita a yankin na Kashmir don bai wa jama'a damar gudanar da Sallar Juma'a bayan da hukumomi suka ayyana dokar hana fita a sakamakon rikicin da ya barke kan raba yankin da kwarya-kwaryar 'yancin gashin kai da ya ke da shi wanda Firaiminista Narendra Modi ya yi.

Mutum sama da dari biyar aka kama ake kuma ci gaba da tsarewa a sanadiyar tashin hankali da ya biyo bayan wannan sanarwar sannan an gano matsalar katsewar hanyoyin sadarwa tun bayan da aka tsaurara matakan tsaro a yankin da al'ummar Musulmi ke da rinjaye.

An dade ana samun rikici a yankin na Kashmir da Indiya ke da iko da shi kafin a wannan makon Firaiminista Narendra Modi ya sanar da janye 'yancin cin gashin kai kamar yadda ya yi alkawaranta a yayin yakin neman zabensa. A baya ya sha zargin Pakistan da amfani da yankin wajen haifara da husuma a tsakanin al'ummar kasar.