Tsauraran matakan tsaro gabanin gangami a Kashmir
August 23, 2019Talla
Kawo yanzu dai mutane 152 ne suka jikkata daga hayaki mai sanya hawaye a Lardin Kashmir mai fama da rikici, tun bayan da jami'an tsaron Indiya suka kaddamar da somame a watan da ya gabata.
Hukumomin Indiyan sun aike da karin rundunar tsaro, tare da haramta wani gangami na al'umma, daura da yanke hanyoyin sadarwa ta wayar salula da ma yanar gizo, a wani mataki na kare aukuwar zanga zanga mai karfi, tun bayan sanar da janye matsayin 'yancin da lardin ke da shi a ranar biyar ga watan Augusta.
Sai dai duk da wadannan matakai, jama'a musamman matasa kan yi jerin gwano a kan titunan babban birnin Lardin watau Srinagar, musamman a ranakku kamar Juma'a su na jifa da duwatsu, matakin da ya janyo martani daga jami'an tsaro.