1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kashe wasu 'yan Mexiko bisa kuskure a Masar

Gazali Abdou TasawaSeptember 14, 2015

Lamarin ya wakana ne lokacin da jami'an tsaron ke kan hanyar farautar wasu mayakan kungiyoyin masu tayar da kasar baya a cikin yankin saharar yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/1GVxz
Soldaten sterben bei Angriff auf Kontrollpunkt
Hoto: picture-alliance/dpa

A Masar jami'an tsaron kasar sun hallaka a bisa kuskure wasu mutane 12 da suka hada da wasu 'yan yawon buda ido 'yan asalin kasar Mexico da kuma wasu Misrawa da ke yi masu rakkiya. Lamarin ya wakana ne lokacin da jami'an tsaron ke kan hanyar farautar wasu mayakan kungiyoyin masu tayar da kasar baya a cikin yankin saharar yammacin kasar a jiya Lahadi.

Ministan cikin gida na kasar ta Masar wanda ya tabbatar da abkuwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce mutanen sun kasance ne a cikin wani yanki inda aka haramta wa 'yan yawan buda ido shiga.

Hukumomin kasar ta Mexiko sun tabbatar da mutuwar 'yan kasar tasu biyu a yayinda wasu biyar suka ji rauni. Kuma tuni shugaban kasar ta Mexiko ya kalubalanci harin bisa kafar sadarwrsa ta Twiter inda kuma ya yi kira ga hukumomin kasar ta Masar da su gaugauta gudanar da bincike a kan lamarin.