Kasashe na ci-gaba da ficewa daga ICC
November 21, 2016Zan yaye kallabin shirin ne da sharhin da jaridar Neues Deutschland ta rubuta game da makomar kotun duniya da ke shari'ar masu manyan laifukan mai matsugunin a birnin The Hague na kasar Netherland. Tun bayan da wasu kasashen Afirka suka ayyana manufarsu na ficewa daga kotun ne dai, wakilan kasashe 124 da suka rattaba hannun kafuwar kotun, suka fara mahawara kan wannan batu a taronsu na shekara shekara da suka kaddamara a wannan Larabar da ta gabata.
Kotun dai na fuskantar barazanar rasa da yawa daga cikin membobinta, ba wai na Afirka kadai ba. Ana zargin kotun ta ICC da rashin adalci kuma wuri na shari'ar shugabannin da basu da gata, duk da cewar shugabannin kasashe musamman na yammacin Turai na aikata laifuka na yaki da ya cancanci gurfanar da sau gaban kotun.
A karon farko dai masu bincike na kotun ta ICC bisa ga tsarin laifukan yaki, sun dubi irin rawar da sojojin Amurka da ma hukumar leken asirin kasar.
Tun daga shekara ta 2003,akwai nau'in cin zarafin bil'adama daban-daban a gidajen kurkuku , ba wai a Afganistan kadai ba, amma har a wani gidan yari na sirri da ke kasashen Poland da da Romania da Lithunia. Tsohuwar gwamnatin George W. Bush ta kirkiri wata mummunar hanya na neman bayanai daga wadanda ake zargi, inda ake azabatar da mutane, kafin shugaba Barack Obama ya soke ofishin a shekara ta 2009.
Ministan tattali da raya kasa ya janye kalaman da ya yi kan mazan Afirka. Wannan shi ne taken labarin da jaridar Die Welt ta rubuta dangane da furucin da Gerd Müller ya yi a birnin Bonn na cewar idan magidanci dan Afirka na da dalar amurka 100,abun da zai kai gida bai taka kara ya karya ba. A cewar Müller dai mazan Afirka sukan kashe kudi kan wasu abubuwa da ba sui da muhimmanci, a maimakon kan harkar ilimin yara da makomarsu da ma iyali baki daya.
A cewarsa dai matan Afirka a daya bangaren na amfani da mafi yawan abun da Allah ya hore musu wajen kula da iyali musamman rayuwar yara, da sauran abubuwanda ake bukata a biya. Tashar talabijin ta ZDF da ke nan Jamus dai ta yayata bidiyon ministan yana wannan furuci ta shafukan sada zumunta na Facebook.
Sai dai Ministan raya kasa na jamus Müller, ya yi amfani da taro kan sauyin yanayi na birnin Marrakesh na Moroko, wajen yin afuwa dangane da wadannan kalamai da ya yi kan mazan afirka. Ya ce abun da ya ke kokarin yi a jawabin nasa shi ne, nuna muhimmancin mata da matasa a makomar Afirka nan gaba.
Mafi yawa daga cikinbankuna kasashen Afirka na fama da rashin isassun jari. Dalili kenan da ya jagoranci durkushewar wasu, wanda kuma hakan na iya durkusar da tattalin arzikin kasashen. Jaridar Neues Deutschland ce ta yi wannan tsokaci a wani sharhi da tayi kan halin tsaka mai wuya da bankunan Afirka ke ciki.
Jaridar ta danganta wannan hali da bankunan ke ciki da tashin gwauron zabi na farashin kayayyakin masarufi da matsalar fari da faduwar darajar kudade da kuma tafiyar hawainiya da tattalin arzikin China ke yi. A yanzu haka dai tattalin arzikin wannan nahiya mai fama da matsaloli na cigaba da fuskantar koma baya.