1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana kada kuri'ar zabe a Moroko

Abdul-raheem Hassan
September 8, 2021

Miliyoyon jama'a na gudanar da zaben 'yan majalisun dokoki da na kananan hukumomi a kasar Moroko, zaben na zuwa a dai-dai lokacin da kasar ke yunkurin farfadowa daga matsin tattalin arziki sakamakon annobar coronavirus.

https://p.dw.com/p/404ug
Wahlen in Marokko | 2016
Hoto: Jalal Morchidi/AA/picture alliance

Kimanin mutane miliyan 18 ne ake sa ran za su kada kuri'unsu a zaben majalisun dokoki mai kujeru 395, da kuma sauran kujerun kananan hukumomi da na yankuna sama da 31,000 a kasar Moroko.

Wannan dai shi ne karo na uku da ake zabe a kasar Moroko, daya daga cikin kasshen da ke arewacin Afirka tun lokacin da aka gabatar da sabon kundin tsarin mulki a shekarar 2011.