Kasar Holland ta aika da makaman kariya ga Turkiya
January 7, 2013Goman motoci ne dauke da karafunan hada makaman kariya suka tashi daga kasar Holland ya zuwaTurkiya a wannan Litanin . Dama dai tun can farko kasar ta Holland ta yi arkaawarin aikawa Turkiya wasu makaman kariya daga barazanar faduwar makamai masu nizamae na kasar Siriya. Rahotani daga kamfanin dillancin labaran Reutres,sun bayana cewar a kalla motacin sulke na sojin kasar Holland 160 ne ke dauke da kayan da za a hadawa domin kafa kariya ga kasar ta Turkiya da ta bukaci kasashen kungiyar NATO da su kare ta daga barazanar faduwar makaman da ake harbawa daga makwabciyarta Siriya. A lokacin da ya kewa manema labarai magana.laftana kanar Marcel Buis na rundunar tsaron Holland,ya ce Siriya nada makan masu cin dogo da gajeren zango wadanda kuma ke iya kaiwa ga wasu mahimman biranen Turkiyar,don haka wajibi ne ga NATO da ta taimaka wa daya daga cikin mambobinta.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mahammad Nasiru Awal