China ta ce za ta yi aiki da gwamnatin Trump
November 17, 2024Shugaban kasar China Xi Jinping ya tabbatar wa takwaransa na Amurka mai barin gado Joe Biden cewa kasarsa a shirye take ta yi aiki tare da gwamnatin shugaba mai jiran gado Donal Trump, domin daidai alaka tsakanin Beijing da Washington wadda ta yi tsami a wa'adin mulkin Trump na farko.
Karin bayani: Trump ya yi wa China gugar zana
A yayin wata ganawa da shugabannin biyu suka yi a daura da taron kasashen yankin Asiya da Pacific da ke gudana a birnin Lima na kasar Perou, Biden da Xi sun yarda cewa bai kamata hamayya da ke tsakanin China da Amurka ta kai ga rikidewa zuwa rikici ba. Shugaba Biden ya ba da misali da wa'adin mulkin da ya yi, inda a cikin shekaru hudu duk da sabanin ra'ayin Amurka da China a game da yakin Ukraine da kuma tankiya kan tsibirin Taiwan kasashen biyu sun taka rawa wajen kyautatuwar zaman lafiya a duniya.
Karin bayani: Amurka da China sun amince da mayar da huldar al'amuran tsaro
Wannan ganawa tsakanin shugabannin manyan kasashen biyu ita ce ta karshe kafin Donald Trump ya karbi madafun iko, wanda a wa'adin mulkinsa na farko takun saka a fannin kasuwanci tsakanin Amurka da China ya yi kamari.