1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Cece-kuce a kan kasafin kudi

July 1, 2024

Matakin majalisun dokokin Najeriya na amincewa bangaren zartarwa ya aiwatar da jerin kasafin kudin kasar kusan guda hudu a lokaci guda, na janyo dagun hakarkari cikin kasar a halin yanzu.

https://p.dw.com/p/4hkY9
Najeriya | Majalisa | Kasafin Kudi | Bola Ahmed Tinubu | 2022 | 2023 | 2024
Shugaban NAjeriya Bola Ahmed Tinubu yayin gabatar da kasafin kudin 2023 a majalisaHoto: Ubale Musa/DW

Majalisun Tarayyar Najeriyar dai, sun bai wa gwamnatin kasar izinin aiwatar da tsohon kasafin kudin da ya gada daga tsohuwar gwamnatin kasar. Sannan kuma zai iya kisan kudin da ke cikin kwarya-kwaryan kasafin kudin na shekarar da ta shude, ko bayan sabon da ya gabatar a shekarar bana da ma wani kwarya-kwaryan kasafi da shugaban yake shirin ya kai gaban 'yan dokar duk dai kafin nan kafin karshen shekarar bana.

Karin Bayani: Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kudin 2024

A tsakanin kasafin kudin kasar guda uku masu mulkin na da karfin ikon kashe abun da ya kai Naira tiriliyan 52, adadi mafi yawa a Najeriyar da take fadin babu kudi. To sai dai kuma tun ba a kai ko'ina ba, yunkurin 'yan dokar na janyo damuwa a Najeriyar da ke cikin matsin tattalin arziki a halin yanzu. Can cikin gida na adawa dai, kokarin kisan jerin kasafin a lokaci guda a tunanin babbar jam'iyyar adawa ta PDP na da babban burin wasoso da dukiya ta 'yan kasar a tunanin Ibrahim Abdullahi da ke zaman mataimakin kakakin jam'iyyar na kasa.

Najeriya | Zanga-Zanga | Tsadar Rayuwa
Zanga-zanga kan tsadar rayuwa a NajeriyaHoto: AP Photo/picture alliance

Ko bayan barazana ta hauhawar farashi cikin kasar da ke tunanin rage tsada ta rayuwa, ana kisan ba gaira cikin tunanin kasafin a fadar Abubakar Ali da ke zaman kwararre a fannin tattalin arzikin kasar. Wannan ne dai karon farkon fari, a shekaru 25 na sake komawa ga tsarin dimukuradiyyar da bangaren zartarwar ke da gatan kisan kudi ba adadi a lokaci guda cikin kasar da ke cin bashi a cikin neman. To sai dai kuma babu laifi a banagren 'yan dokar na amincewa da sabon tsarin, a fadar Hoin Inusa Abubakar da ke zaman tsohon dan majalisar wakilai ta kasar.

Karin Bayani: Gwamnatin Najeriya ta fadada hanyar samun kudin shiga

Ana dai zargin shi kansa daukar matakin, a matsayin wani ci gaba na danyen ganye a bangaren zartarwar da masu doka na kasar. Ci gaban kuma da ya kalli kau da kai a banagren zartarwar tare da kyale masu yin dokokin kara yawan kasafin kudi na batarwarsu ya zuwa Naira miliyan dubu 344 daga miliyan dubu 228 da yake a shekarar da ta shude.