1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karshen sabanin Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa

Suleiman Babayo ZUD
July 15, 2024

Gwamnatin Najeriya ta kulla yarjejeniyar kawo karshen takaddamar tafiye-tafiye na hana 'yan kasar visan zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa.

https://p.dw.com/p/4iLMN
Jiragen sama
Jiragen samaHoto: AP

Kasar Najeriya ta cimma yarjejeniya da Hadaddiyar Daular Larabawa domin dawo da tafiye-tafiye tsakanin kasashen biyu, inda matakin zai kawo karshen hana 'yan Najeriya visa zuwa kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa tun shekara ta 2022.

Karin Bayani: Emirates ya janye barazanar da ya yi wa Najeriya

Ministan yada labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya tabbatar da cimma wannan yarjejeniya tsakanin kasashen biyu na Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa. Ministan ya ce daga wannan Litinin an koma bai wa 'yan Najeriya visa na zuwa kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa, da ma tun farko babban bankin Najeriya ya biya jiragen saman kasashen duniya kudin da suke bin kasar kimanin Dalar Amirka milyan 137.