Gwaraza masu dakile harin ta'addanci
August 24, 2015Shugaba Francois Hollande ya bada lambar yabon ga wadannan mutane hudu wanda suka hada da Spencer Stone da Alek Skarlatos da Anthony Sadler wadanda Amirkawa ne da kuma Chris Norman dan Burtaniya bisa jarjircewa da suka yi wajen dakile harin da ake zargin wani matashi dan kasar Maroko Ayoub El Khazzani ya yi a cikin jirgin kasa lokacin da suke hanyarsu ta zuwa birnin Paris na Faransa.
Shugaban Hollande ya ce jarumtar mutanen hudu abin a yaba ne, shi ne ma ya sanya Faransa din yanke hukuncin basu lambar girma mafi daraja da ake badawa a kasar.
Ya ce "Mutumin na dauke da makamai da zai iya amfani da su wajen haddasa mummunar ta'asa, ba don wadannan mutane sun yi wannan yunkuri ba ta hanyar sayar da ransu to Allah kadai ya san irin abinda zai faru".
Shugaba Hollande ya kara da cewa duniya baki daya na alfahari da wannan kokari da mutanen suka yi kuma ya ce hakan zai taimaka wajen zaburar da sauran jama'a wajen yin abu makamanci wannan don samun magance kai hare-hare.
Da ya ke tsokaci kan wannan namijin kokari da suka yi, guda daga cikin mutanen Anthony Sadler ya ce zama haka ba tare da yunkuri na murkushe masu son aikata ta'addanci ba zai haifawa duniya komai ba sai cizon yatsa.
Ya ce "Buya ko ja da baya ba zai haifa mana komai ba. Da ba mu yunkura ni da abokaina ba to da dan bindigar ya yi nasara don haka ina rokon mu da mu yi wani abu da zarar mun fuskanci ana kokari na kai harin ta'addanci".
Mutane da dama ciki kuwa har da Firaministan Belgium Charles Michel da jakadan Amirka a Faransa Jane Hartley ne suka halarci wannan taro a fadar ta Elysee, har ma jakadar Amirka din ke cewar ya zama wajibi a jinjinawa wadannan gwarzaye.
"Muna amfani da kalma ta gwarzo sosai amma babu wani loakci da ya kamata mu yi amfani da ita fiya da yanzu. Wadannan mutane ba za su so a ce musu gwarzaye ba saboda irin kawaici da kankan da kai da suke da shi to amma fa babu ko shakka gwarzaye ne.
To yayin da ake gudanar da bikin karrama wadannan mutane hudu, su kuwa jami'an tsaron Faransa na ci gaba da bicike kan wannan matashi wato Ayoub El Khazzani kuma bayanai sun nuna cewar a gobe ne hukumomi za su yi karin haske game da daukar matakin shari'a a kansa.