1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin wasanni: Bitar wasannin Lig na tarayyar Jamus

Suleiman Babayo AMA
August 23, 2021

A cigaba da wasannin Bundesligar Jamus an fafata tsakanin kungiyoyin kwallon kafa, a daidai lokaci guda kuma masana na fashin kan wasan cin kofin kwallon kafa na Afirka da za a yi a Kamaru.

https://p.dw.com/p/3zNPI
Bundesliga | Bayern - Köln
Karawa tsakanin 'yan wasan Bayern - Köln a gasar BundesligaHoto: Sven Hoppe/dpa/picture alliance

A wasannin lig na Bundesliga na tarayyar Jamus da aka kara a karshen makon jiya kungiyar Leipzig 4 Stuttgart 0 Eintracht Frankfurt 0 Augsburg 0 Hertha Berlin 1 Wolfsburg 2 Bochum 2 Mainz 0 Hoffenheim 2 Union Berlin 2 Bayern Munich 3 Cologne 2. Mun kawo maku kai tsaye wasan da aka kara tsakanin Freiburg Borussia Dortmund 2-1.

A wasannin lig na La Liga na Spain Atlantiko Bilbao ta tashi kunnen doki, 1 da 1 da kungiyar Barcelona, haka Levante da Real Madrid sun tashi 3 da 3. Yayin da a wasannin liga na Premier na Ingila, Chelsea ta bi Arsenal gida ta doke ta 2 da nema, Southampton ta tashi 1 da 1 da kungiyar Manchester United, sannan Aston Villa ta doke Newcastle 2 da nema.

Wasannin Olympics na masu bukata ta musamman

Parapan Am Games Toronto  David Eng
'Yan wasan Paralympic na tseren keke Hoto: picture-alliance/empics/N. Denette

Daga wannan Talata mai zuwa 24 ga watan Agusta ake fara wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya, Olympics, na masu bukata ta musamman a birnin Tokyo na kasar Japan, kuma za a yi wasannin zuwa ranar 5 ga watan gobe na Satumba, a gaba daya makonni biyu za a shafe ana fafata wasannin.

Tuni masana da sauran masu sharhi kan harkokin wasanni suka fara fashin baki kan gasar neman cin kofin kwallon kafa na kasashen Afirka da za ta gudana a kasar Kameru a shekara mai zuwa ta 2022, inda a makon da ya gabata aka fitar da jadawalin fafatawa tsakanin kasashe, kuma wakilinmu Nasiru Salisu Zango na dauke da rahoto daga birnin Kano na Najeriya.