Karin kudaden haraji ga kayayakin kamfanonin Amirka a China
August 23, 2019Talla
Tuni dai shugaban ya bukaci kamfanonin Amirka da su dauki wasu kwararan matakai kan kayan da suke samarwa a China, inda Donald Trump ya ce Amirkar ba ta bukatar China domin tana iya tafiya da ita ko ba ita.
A baya dai kasar China ta bayyana anniyarta ta kara kudade kimanin dala biliyan 75 na kudin fito ga daukacin kayayakin da ke shiga kasar da su daga kasar Amirka, matakin da kuma ya kara haifar da zaman doya da manja da aka jima ana fuskanta tsakanin kasashen biyu.