1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Karfafa dakaru a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Suleiman Babayo MAB
March 13, 2021

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da tura karin dakaru sojoji da 'yan sanda kimanin 3,700 zuwa kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/3qabz
Zentralafrikanische Republik UN Soldaten in Bangui
Hoto: UN/RCA

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da tura karin dakaru sojoji da 'yan sanda kimanin 3,700 zuwa kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, domin kare samun tabarbarewar tsaro da ake gani a kasar na karuwa tun bayan zaben shugaban kasa na watan Disamba da ya gabata. Karkashin sabon kudiri sojojin da ke aikin kiyaye zaman lafiya za su kai kimanin 14,400 sannan 'yan sanda zuwa 3,020.

Tun a watan jiya babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci ganin an amince da wannan sabon kudiri.

A wannan Lahadi ake zaben zagaye na biyu na zaben 'yan majalisar dokokin kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula, da gwamnatin Shugaba Faustin Archange Touadera ta kwashe watanni tana fuskanta daga 'yan tawaye masu dauke da makamai.