1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar hana fita a Kamaru

Zainab Mohammed Abubakar
September 30, 2018

Shugaba Paul Biya na Kamaru ya bayyana cewar, kasarsa ta cimma nasarar yakar Boko Haram. Wannan dai shi ne karon farko da ya gabatar da irin wannan sanarwa, shekaru hudu bayan kaddamar da yaki a kan mayakan na sakai.

https://p.dw.com/p/35jcE
China Peking - Kameruns Präsident Paul Biya
Hoto: picture-alliance/AP Photo/L. Zhang

Ya yi wannan furuci ne a jawabinsa na yakin neman zabe a yankin arewa mai nisa, wanda ke zama ziyararsa ta farko a yankin tun daga shekara ta 2012.

Mai shekaru 85 da haihuwa, kuma daya daga cikin dottijan da ke mulkin sai madi ka ture a Afirka, Biya na shugabancin Kamarun ne tun daga shekara ta 1982, kuma bisa dukkan alamu shi ne zai lashe zaben na ranar 7 ga watan Oktoba, kasancewar 'yan adawa sun gaza fitar da dan takara mai karfi.

Yanzu haka dai kasar na fama da matsalar tsaro, daura da rigingimun na fafutukar neman 'yancin cin gashin kai daga bangaren 'yan awaren kasar masu magana da harshen turancin Ingilishi, da ke yankin Kudu da Arewa maso Yammaci.

Inda ko a yau (Lahadi) mahukuntan Kamarun sun sanar da kafa dokar hana fita na tsawon sao'i 48, a jajibiren bukin cika shekara guda da ayyana 'yancin kai yankin na 'yan aware.