Kamaru: Cikas a kan sha'anin makarantu
September 25, 2023A halin yanzu iyayen yara na kokawa sakamakon yajin aikin Malaman makarantun sakandare a Kamaru, yau makwanni uku kenan da Malaman makarantun sakandare da suka tsunduma yajin aiki a fadin kasar inda suke neman gwamnati ta kyautata albashi da sauran hakkokin a matsayinsu na ma’aikata. Kamar yadda su ka yi a bara. Wannan matsala dai ta yajin aikin Malaman makarantu sakandare a Kamaru ta zama ruwan dare gama gari kuma ya zama karan tsaye ga karatun yara wanda basu san hawa ba su san sauka ba.
Gwamnonin wasu yankuna na Kamaru na yi barazana ga malaman da ba su koma bakin aikinsu ba
Bayan makwanni uku da yajin aikin Malaman makarantun sakadaren a Kamaru babu abin da ya sauya sai dai barazanar da suke Malaman ke fuskanta daga wasu gwamnonin yankunan Kamaru. Shekarar makaranta ta 2023-2024 na iya fuskantar cikas sakamakon yajin aikin malaman makarantun gwamnati a Kamaru. Malan sun nuna cewar idan gwamnati ba ta mutunta alkawuran da ta dauka ba, a shirye su jagoranci yajin aikin har zuwa lokacin da suka yanke shawarar duba matsalarmu da gaske, a wannan karon malaman sun kuduri aniyar, nuna cewa wannan gwamnati ba ta da muradin magance matsalolinsu. Yajin aiki ya riga ya gurgunta harkar ilimi a bara. Matakan da gwamnati ta dauka sun kai ga dakatar da yajin aikin. Sai dai a wannan sabuwar shekarar a cewar kungiyoyin makarantu, an kori malamai.
Malaman sun nace kan cewar babu gudu babu ja da baya sai gwamnati ta biya musu bukatunsu
Tun daga watan Fabrairun 2022, malamai a Kamaru sun tashi tsaye don yin tir da wasu munanan ayyuka da ba sa girmamakoyarwa da kuma lalata al'ummar ilimi gaba ɗaya. ga matsalolin da malamaisuka taso abin takaici, ba a aiwatar da wadannan umarni ba har zuwa wannan rana, don haka muna mayar da wadannan abubuwa guda biyu a kan tebur a kan sake duba matsayin malaman makaranta a matsayin ma'aikacin gwamnati.