Hukumomin Kamaru sun ja kunnen 'yan adawa a kasar
September 21, 2020Talla
Gamayyara jam’iyyun adawan kasar Kamaru karkashin jagorancin madugun adawa Maurice Kamto sun sha alwashin kawo karshen mulkin Shugaba Paul Biya na sama da shekaru 38.
Kamto da magoya bayansa sun shirya kaddamar da wata gagarumar zanga-zanga da tuni ake kwatantawa da irin wanda ya samar da juyin mulki a kasar Mali.
Wannan shi ne karon farko da mulkin Shugaba Paul Biya ke fuskanta barazana daga bangaren adawa, wanda tuni masana ke ganin akwai bukatar a dauki mataki don gudun aukuwar abin da ya faru a Mali.
A gobe Talata (22.09.2020) ne aka shirya gudanar da zanga-zangar.