An kama jagoran adawan kasar Kamaru
January 29, 2019A wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar a wannan Talata, ta zargi gwamnatin Yaounde da neman kawar da jagoranta Maurice Kamto wanda ke ci gaba da kalubalantar sakamakon zaben Shugaba Paul Biya a matsayin shugaban kasa, tare da bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben.
Yanzu haka dai ko baya ga Kamto da akwai wasu magoya bayan 'yan adawa 117 da ake tsare da su, ciki har da, Alain Fogue, ma'ajin kudin jam'iyyar adawar ta MRC, da Paul Eric Kingue tsohon daraktan yakin neman zaben dan takarar adawar, da kuma wani mawaki mai suna Valsero da ke goyon bayan Kamto.
A ranar Asabar da tagabata ne dai jam'iyyar ta kira zanga-zanga a dukkanin fadin kasar domin nuna rashin amincewa da tazarcen Shugaba Paul Biya dan shekaru 85 da haihuwa wanda kuma da ya shafe tsawon shekaru 36 a madafan ikon kasar.