1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matsalolin tattalin arziki a Libiya

Zulaiha Abubakar SB
February 15, 2020

Firaminista Fayez al-Sarraj na Libiya ya nuna damuwa game da sake afkawar kasar cikin matsalar tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/3Xpn1
Libyen Symbolbild | UN-Sicherheitsrat Resolution zur Unterstützung der Beschlüsse der Libyen-Konferenz in Berlin
Hoto: picture-alliance/Xinhua/A. Salahuddien

Gwamnatin da Majalisar Dinkin dunya ta amince da ita a kasar Libya karkashin ikon firaminisra Fayez al-Sarraj ta bayyana cewar kasar za ta fuskanci kalubale a kasafin kudi wanda zai haifar sakamakon toshe cibiyoyin hakar mai da mabiya kwamanda Khalifa Haftar suka yi a kasar.

Hasashen ya biyo bayan kiraye-kirayen da masu shiga tsakanin a rikicin kasar suke yi wa 'yan tawayen da ke gabashin kasar kan muhimmancin sulhu domin Libiya ta farfado daga rikicin da ta afka tun bayan mutuwar Marigayi Shugaba Moammar Ghaddafi.