Kalubalen da ke a gaban Angela Merkel
September 28, 2017Talla
Za a dai kwashe kwanaki shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel tana tattaunawa da jam'iyyun siyasar, misali FDP da kuma ja'imyyar masu fafutukar kare muhali watau Grüne wajen kafa gwamnati. Sai dai kuma akwai sabani tsakanin jam'iyyun a game da batun bakin haure da na kungiyar EU, abin da ake gani zai kasance mai wahala ga shugabar gwamnatin wajen samun abokanan tafiya.