Kakakin majalisar dokokin Gabon ya yi murabus
March 31, 2016Talla
Kakakin majalisar dokokin Gabon Guy Nzouba Ndama ya yi murabus daga mukaminsa sakamakon abin da ya kira shishshigi da bangaren zartaswa ke yi wa harkokin majalisa.
A ranar Talata da ta gabata jam'an 'yan sanda suka kutsa cikin majalisar da ke da mazauninta a Libreville fadar gwamnatin kasar inda suka hana ma'ajiyin majalisar yin aiki.
Wasu daga cikin 'yan majalisa da ke goyon bayan kakaki Nzouba Ndama sun bukaci jam'iyar da ke mulki ta tsayar da wani dan takara, saboda Shugaba Ali Bongo bai tsinana wa kasar komai ba a wa'adinsa na mulki. Sai dai tuni aka raba uku daga ciki da mukaminsu.