1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ginin makaranta ya halaka dalibai a Jos

Abdullahi Maidawa Kurgwi LMJ
July 12, 2024

Rahotanni daga jihar plateau a Najeriya, sun nunar da cewar masu aikin ceto na kokarin zakulo yara dalibai da gini ya rufta a kansu, a daidai lokaci da suke tsaka da zana jarrabawa.

https://p.dw.com/p/4iEx3
Najeriya | Plateau | Jos | Gini | Makaranta | Saint Academy | Dalibai
Ci gaba da kokarin ceto wadanda gini ya rutsa da asu a birnin Jos na NajeriyaHoto: NEMA Nigeria/X

Makrantar da ake kira Saint Academy na unguwar Busa Buji ne, a  garin jos fadar gwamnatin jihar ta Plateau. Nan take dai a jama'a suka kai dauki, domin ceto wadanda ginin ya rutsa da su kafin zuwan hukumomin bayar da agaji. Madam Anna Onyebushi na da yarinya a makarantar ta Saint Academy, ta shaidawa DW cewa ta shiga mawuyacin hali da samun labarin ruftawar ginin kafin ta gano 'yar ta ba ta cikin ginin lokacin da ya rufta. Duk da daukin da al'umma suka fara kai wa, yara da dama da kuma malamai ne aka tabbatar sun raunuka. Duk wani kokari na samun karin bayani daga jamai'an Hukumar ba da Agajin Gaggauwa ta NEMA da DW ta yi dai, ya ci tura. Suma a nasu bangaren, hukumomin jihar ta Plateau a ba su fitar da alkaluma na adadin daliban da suka rasa rayukansu ko suka samu raunuka ba. Sai dai yayin ziyara da wakilin DW ya kai asibitocin da aka garzaya da wadanda abun ya rutsa da su, ya shaidar da ganin gawarwaki sama da biyar da kuma mutanen da dama da suka jikkata. Ana dai fargabar adadin wadanda suka rasa rayukansu ka iya karuwa, kasancewar ana ci gaba da lalubo mutane a karkashin ginin da ya rufta.