Amirka: An rantsar da Joe Biden
January 21, 2021Sabon shugaban kasar ta Amirika Joe Biden ya fara ne da soke wasu daga cikin dokokin wucin-gadi da tsohon shugaban da ya gada Donald Trump ya rattabawa hannu. Daga cikin dokokin da Biden din ya soke sun hadar da dokar da ta hana 'yan wasu kasashen Musulmi shigo Amirkan da ta gina katangar da za ta raba iyakar kasar da Mexico.
Biden wanda ya yi alkawarin kawo sauyi a dangantakar kasar da kasashen ketare, ya kuma ayyana sake mayar da Amirka cikin yarjejeniyar muhalli ta birnin Paris da kasashen duniya suka cimma wadda Trump ya fitar da kasar daga cikinta, tare da bayyana cewa Amirkan za ta ci gaba da yin aiki tare da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, wanda hakan zai taimaka masa a burinsa na yin yaki da annobar cutar corona a ciki da wajen kasar. Yanzu dai an zuba idanu domin aga sauran matakan da Biden zai dauka, ciki kuwa har da tasirin da da ake hasashen gwamnatinsa za ta yi a Yankin Gabas ta Tsakiya.