Jirgin yakin Saudiya ya fadi a Yemen
April 18, 2017Talla
A yanzu dai dakaraun hadin gwiwa da ke yaki a Yemen sun kaddamar da bincike dan gano musabbabin faduwar jirgin mai dauke da mutane 12. Mayakan Houthi sun kwace iko da babban birnin kasar ta Yemen Sana'a a shekara ta 2014, wannan ya sa kasar Saudiya ta fara kai hare-hare babu kakkautawa a kan mayakan na Huthi a shekara ta 2015. Amma daga baya-bayannan sojojin Yemen da ke samun goyon bayan Saudiya na samun galabar inda suke maido yankuna da dama ciki har da kudancin birnin Aden karkashin ikon gwamnati.