Jirgin saman Emirates ya kama wuta bayan ya sauka a Dubai
August 3, 2016Wani jirgin sama samfurin Boeing 777 na kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Emirates da ya tashi daga Indiya ya yi hatsari lokacin da ya zo sauka a Dubai. Dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin su kimanin 300 sun tsira kuma suna cikin koshin lafiya a cewar wata sanarwar gwamnatin kasar ta Daular Larabawa. Jirgin ya kama da wuta ne lokacin da yake kokarin sauka a Dubai. Dr Girisankal Ganga-Dhakan, matarsa na cikin jirgin cewa ya yi.
"Matata ta kira awa daya baya ta ce a lokacin da suke sauka jirgin ya kama da wuta, amma sun tsallake rijiya da baya. Na kadu da jin labarin."
Rahotanni sun ce akalla inji daya na jirgin ne ya kama da wuta, yanzu haka kuma an dakatar da tashi da saukar jiragen sama a filin jirgin saman na Dubai da ke da muhimmanci a zirga-zirgar jiragen sama tsakanin kasa da kasa.