Jirgin sama ya kama da wuta bayan hadari a Tokyo na Japan
January 2, 2024Wani jirgin sama mallakin kasar Japan ya kama da wuta a filin jirgin saman Tokyo-Haneda, inda wasu kafafen yada labarai ke nuna yiwuwar karo da wani jirgin na daban. Tashar talabijin ta NHK mallakin gwamnati ta ruwaito cewar an kwashe akasarin daruruwan fasinjojin da ke cikin jirgin saman, amma ana ci gaba da neman mutane biyar da suka bace. Wannan jirgin kirar Airbus ya taho ne daga Sapporo da ke yankin arewacin Japan a lokacin da ya bugi wani jirgin mallakin masu gadin gabar tekun Japan. Amma kawo yanzu babu bayani game da musabbabin hadarin.
Karin bayani: Sama da bakin haure 60 sun sake mutuwa a hadarin jirgin ruwa
Ba a dai cika samun hatsarin jiragen sama a kasar Japan ba. Sai dai hadari mafi muni ya faru ne a shekarar 1985, inda ya kashe mutane 520. Wannan hadarin ya zo ne kwana guda bayan ibtila'i na girgizar kasa da ya afku a yankin Noto da ke tsakiyar kasar Japam, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 48.
2024-01-02T10:43:26Z UTC