1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 76 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa

Abdul-raheem Hassan
October 10, 2022

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kimanin mutane 85 ne ke cikin jirgin a lokacin da ya kife a yankin Kudu maso yammacin kasar da ambaliyar ruwa ta yi barna.

https://p.dw.com/p/4HyE0
Kifewar jirgin ruwa a Najeriya
Hoto: AP/picture alliance

Rahotanni daga jihar Anambara da ke kudancin Najeriya, na cewa mutane 76 sun mutu bayan nutsewar jirgin ruwa sakamakon ambaliya a yankin Okbaru. Ofishin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce mutane 85 ne ke cikin jirgin lokacin da ya kife a ranar Juma'a.

A ranar Asabar hukumomi sun ce mutane 10 sun mutu 60 sun bace, hukumar agajin gaggawa ta jihar ta ce an ceto mutane 15 a daren ranar Asabar. Yanzu haka dai Shugaba Buhari ya umarci hukumomin agajin gaggawa zuwa yankin da hatsarin ya auku.

Yanzu haka dai fiye da mutane 300 sun mutu sakamakon amabaliya  yayin da gidaje sama da 100,000 suka lalace sakamakon ambaliya na baya-bayan nan wanda shi ne mafi muni da kasar ta gani tun 2012 a cewar hukumar NEMA.