Jawabin Scholz a majalisar dokoki
November 14, 2024Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da yanzu haka ke fuskantar matsin lamba a siyasar cikin gida, ya nemi hadin kan 'yan majalisar dokokin kasar don yin aiki tare, domin samun nasarar babban zaben kasar da za a gudanar a farkon sabuwar shekara mai kamawa ta 2025. Mr Scholz ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar ta Bundestag na ranar Laraba, wanda ya fuskanci zazzafar muhawara da musayar ra'ayi.
Karin Bayani: An saka ranar zabe a Jamus
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya halarci zaman majalisar ne don gabatar da tsare-tsaren jadawalin gudanar da babban zabe mai zuwa, sannan kuma a gefe guda ya kare matakin da ya dauka na korar ministan kudi Christian Lindner, yana mai cewar babu ta yadda za a yi ya nade hannunsa yana kallon yadda wasu ke watangaririya da al'amuran da suka shafi sha'anin kudaden da Jamus ke kashewa a fannin tsaro.
Tun a shekarar 2021 Olaf Scholz na jam'iyyar SPD ke jagorantar kasar Jamus, karkashin tafarkin hadakar jam'iyyun FDP da kuma Greens, kafin gayyar ta watse a makon da ya gabata. Yanzu kallo ya koma sama, don ganin wanda zai zama rabagardama a zabe mai zuwa, tuni ma babbar jam'iyyar adawa ta CDU ta fara fafutukar yada manufofinta a kokarinta na ganin ta zama zakaran gwajin dafi, inda jagoranta a majalisar ta Bundestag Friedrich Merz ya mayar da zazzafan martani ga shugaba Scholz, inda ya nuna rashin iya shugabanci daga bangaren shugaban gwamnatin.
Tuni dai masu neman darewa kan kujerar shugaban gwamantin Jamus suka fara tallata kansu a majalisar, cikinsu har da jagorar jam'iyyar AFD mai kyamar baki Alice Weidil, da kuma jagoran jam'iyyar Greens kuma ministan tattalin arziki Robert Habeck.