Jaridun Jamus: Koma baya ga kotun duniya ta ICC
April 8, 2016A sharhin da ta rubuta kan hukuncin jaridar Neue Zürcher Zeitung ta fara ne da cewa koma baya ga fannin shari'a na kasa da kasa. Kotun duniya ta ICC ta dakatar da shari'ar da take wa mataimakin shugaban Kenya William Ruto saboda dalilai da suka hada da angizon siyasa. Ruto dai an zarge shi da hannu a mumunnan rikicin da ya biyo bayan zaben kasar Kenya na shekarar 2007 inda aka kashe daruruwan mutane sannan wasu dubbai suka tsere daga muhallinsu. Kotun ta ICC dai ta ce ba zai yiwu a yi shari'a ta adalci ba domin ko dai ana yi wa shaidu barazana ko kuma an ba wa wasunsu hanci. Akalla mutane 16 daga cikin shaidu 42 sun janye daga ba da shaida saboda dalilai na tursasawa da kuma tsoron daukar fansa kansu, wasu kuma sun karbi toshiyar baki. Janye tuhumar dai inji jaridar tamkar wani naushi ne ga ICC da kuma ke saka ayar tambaya kan yin adalci musamman ga wadanda aka ci zalinsu.
Badakalar sojojin kiyaye zaman lafiya
Mataimaka sun rikide sun zama masu cin zarafi, inji jaridar Süddeutsche Zeitung a sharhin da ta yi game da zarge-zargen cin zarafi da gallaza wa jama'a da ake ci gaba da yi wa sojojin Majalisar Dinkin Duniya a Kwango.
Jaridar ta ce ministan shari'ar Kwango Alexis Thambwe ya yi kira da a yi adalci dangane da shari'ar da ake wa sojojin Majalisar Dinkin Duniya su uku a kasar yana mai cewa ba za su yarda wasu kalilan sun bata sunan ilahirin dakarun sojin kasar ba. Sai dai kokarin wanke sunan sojin kasar ba shi ne mataki mafi dacewa ba, domin su ma dakarun tawaye a gabashin kasar sun aikata ta'asa. Sai dai a wannan karon zargin da ake yi ya bambamta domin sojojin uku suna aiki ne karkashin lemar Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Ana zarginsu da yi wa mata da 'yan mata fyade. Tuni dai aka tuhumi abokan aikinsu 18 a wata shari'a ta dabam. Dukkansu sun musanta zargin.
Matakan murkushe 'yan adawa a Kwango
Shugaban Jamhuriyar Kwango Denis Sassou-Nguesso na amfani da sojoji wajen kare nasarar zaben da ya samu mai cike da rudani, dubban mutane sun tsere inji jaridar Die Tageszeitung wadda ta mayar da hankali kan matakin karfi da shugaban ke dauka don murkushe duk wani boren adawa da ci gaba da rike madafun iko da yake yi. Jaridar ta ce tun da sanyin safiyar ranar Talata aka girke rundunonin soji kan manyan hanyoyi a unguwannin da ke zama tungar 'yan adawa da ke Brazzaville babban birnin kasar, bayan wani gumurzu a ranar Litinin tsakanin wasu 'yan bindiga da ba a tantance su ba. Fadan dai ya tilasta dubun dubatan mutane tserewa daga yankin.